About Kundin Tarihi - Aminu Daurawa Part 2 MP3 Offline
Assalamu Alaikum Yan Uwa Maza da Mata,
Muna dauke da manhaja wadda ke dauke da Karatun Kundin Tarihi Tare da Malam Aminu Ibrahim Daurawa.
Wannan Application Kyauta ne dominku 'yanuwa Hausawa Musulmi.
Kuma baya bukatar internet ko data ko WiFi
Sannan free neh, kuma akwai sauti mai inganchi
aminu Daurawa kundin tarikhi
Mal. amin Ibrahim daurawa
Malam Aminu Daurawa offline kundin tarihi
Kundi irin na tarihi tare da Sheikh Daurawa Kano
Offline mp3 aminu daurawa kundi
Mallam Amin Tarihi without internet connection
Domin wadansu karatuttukan na HAUSA kamar Qur'an Tafseer by Sheikh Jaafar Mahmud Adam duba cikin Play store.
Wannan App kashi biyu ne, akwai part 1 da kuma 2. Wannan shine na farkon. Kashi na biyu yana cikin wannan store.
Idan kana/kina da shawara game da wannan App na Malam Aminu Ibrahim Daurawa wato Kundin Tarishi yi amfani da email din developer ka/ki turo da sakonka/ki.
Wannan App baya bukatar data ko wifi Connection, yana aiki ne Offline. Daga kayi downloading sa to shi kenan a ko da yaushe zaka iya amfani dashi domin sauraron karatun Kundin Tarihi.
Baka bukatar tura karatun cikin wayarka/ki. Yin hakan zai ci waje mai yawa daga memory din wayarka/ki. Amma idan kayi amfani da wannan App to size din zai zama dan kadan sannan kuma baka bukatar dube-duben files. Gaba daya Kundin Tarishin yana cikin wannan App a shirye.
Idan ka/kin ji dadin wannan App, inason ku tayani da Addu'ar samun shiriya da kuma yardar Allah subhanahu wata'alaa. Allah ya shiryemu gaba daya ya kuma sanyamu cikin masu babban rabo da kuma kyakkyawan lada wato Aljannah Ameen Ameen.
Allah ya saka ma Malam Aminu Ibrahim Daurawa da AlkhairinSa Ameen.
Nagode da ka/ki duba wannan App nawa!
Ku huta lafiya.
dan daga cikin tarihin Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa,
TARIHIN SHEIKH AMINU DAURAWA KANO :-
Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifina shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa,
bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala. Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne:
1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa.
8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a wajensa. Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji qansa da rahama!